FatimatuzZahra (AS) tana cewa : Duk wandaya kusanta da Allah yana maitsarkake ibadarsa Allah zai saukar masada mafificiyar maslaharsa (ya biya masa mafificiyarbukatarsa)
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: لَو اُتِيتُ بِشابٍّ مِن شَبابِ الشِّيعَةِ لا يَتَفَقَّهَ (في الدِّينِ) لَأَدَّيتُهُ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Da za a zomun da wanisaurayi daga samarin shi’a dabaya nemanilimin addini da na ladabatarda shi.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: فَضلُ الشّابِّ العابِدِ الَّذي تَعَبَّدَفي صِباهُ عَلَى الشَّيخِ الَّذي تَعَبَّدَبَعدَ ما كَبُرَت سِنُّهُ كَفَضلِ المُرسَلينَ عَلى سائِرِ النّاسِ.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Fifikon saurayi maiibada wanda yake bauta a kuruciyarsaakan tsohon da yake bautabayan ya manyanta kamar fifikonmanzanni ne akan sauran mutane.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ اللهَ يُحِبُّ الشّابَّ الَّذي يُفنيشَبابَهُ في طاعَةِ اللهِ عزّوجلّ
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Allah yana son bawan da yakekarar da samartakarsa wajan bin (bautar) Allah (SWT) .
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ الله تَعالى يُباهي بِالشّابّ ِالعابِدِ المَلائِكةَ ، يَقولُ : اُنظُرُواإلى عَبدي! تَرَكَ شَهوَتَهُ مِن أجلي .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Allah yana alfahari da saurayimai bauta ga mala’iku , yana cewa : ku duba bawana! ya bar sha’awarsasaboda ni.
قال امام صادق عليه السّلام: قالَ رسولُ اللهِ صلّى الله عليه و آله : ليسَ مِنّي مَنِ استَخَفَّ بِالصَّلاةِ ، لايَرِدُ عَلَيَّ الحَوضَ لا وَاللهِ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Wanda ya wulakanta salla ba ya dagacikinmu, ba kuma zai zotafkina ba , a’a sam Wallahi!.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: النَّظَرُ في وَجهِ العالِمِ حُبّاً لَهُ عِبادَةٌ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Duba zuwa ga fuskar malamidomin so a gare shi ibada ne.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: خَيرُ النّاسِ منِ انتَفَعَ بِهِ النّاسُ
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Mafificin mutane wanda mutane suka amfana dashi.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ أبخَلَ النَّاسِ مَـن بَخَلَ بـِالسَّـلامِ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Hakika mafi rowarmutane shi ne wanda yayi rowa dasallama.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: لينوا لِمَن تُعَلِّمون َولِمـَن تَتَعَلـَّمـونَ مِـنـهُ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ku tausasawa wanda kukekoyarwa da kuma wanda kukekoya daga gare shi.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: أحسِن إلى مَن أساءَ إلَيكَ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ka kyautata wa wandaya munana maka.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: المُسلِمُ مَن سَلِمَ المُسلِمونَ مِن لِسانِهِ ويَدِهِ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Musulmi shi ne wanda musulmi suka kubuta dagaharshensa da hannunsa.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنّي أمزَحُ ولا أقولُ إلّا حَقاً .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ni inayin raha amma ba na fadasai gaskiya.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: النَّظَرُ سَهمٌ مَسمومٌ مِن سِهامِ إبليسَ فَمَن تَرَكَها خَوفاً مِنَ اللهِ أعطاهُ إيماناً يَجِدُ حَلاوَتَهُ في قَلبِهِ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Kallo (zuwa gaharam) kibiya ce daga kibiyoyin Iblis duk wanda yabar shi saboda jin tsoron Allah, zai ba shi imanin dazai ji dadinsaa zuciyarsa.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ اللهَ تَعالىيُحِبُّ الشّابَّ التّائِبَ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Allah yanason saurayi mai tuba.
قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: اِعمَل لِدُنياكَ كَأنَّكَ تَعيشُ أبَداً ، وَاعمَل لِآخِرَتِكَ كَأَنَّكَ تَموتُ غَداً.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ka yi aiki don duniyarka kamar ka rayu harabada, ka yi aiki don lahirarka kamar ka mutu gobe.
قال رسول الله (ص) : خير لهو المؤمن السباحة ، وخير لهو المرأَة المغزل
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Mafificin wasan mumini shi ne iyoa ruwa, mafificin wasan mace shi ne saka.